إنما وليكم الله ورسوله والذين آمنوا الذين يقيمون الصلاة ويؤتون الزكاة وهم راكعون
Ma'ana:
Abin Sani kawai, Majibincin ku Allah, Manzon Sa, da Wadanda suka yi Imani,Sune Wadanda ke tsayar da Sallah kuma suna bada zakka a lokacin suna ruku'i.
A wajan 'Yan Shi'a Imamiyyah wannan Ayar ta sauka ne akan Imam Ali (A.S) lokacin da ya mika zoban sa a halin ruku'i ga Almijirin da ya shigo Masallaci yana bara. Wasu Malama Ahlussunnah da suka tafi akan cewa ta sauka ne lokacin da Imam Ali ya bada Sadakar zoben sa ga Almijiri, akwai:
1-Qadhi Iiji, cikin Littafin sa "Mawaqif fi Ilmil Kalam" Shafi na 45
2-Sharif Jarjani, cikin Littafin sa "Sharhul Mawaqif" Juz'i na 8, Shafi na 360
3-Qushji, cikin littafin sa "Sharhut tajriid" Shafi na 368.
Yazo cikin tafsirin ibn Abi Hatim, juz'i na 4, shafi na 1162, wanda sanadin sa ya tuke akan Salmata bin Kahil, ya ce:
تصدق علي بخاتمه وهو راكع فنزلت الآية (إنما وليكم الله ورسوله...)
Ma'ana
Aliyu ya yi sadaka da Zoben sa alokacin da yake ruku'i, sai Allah Ya saukar da Ayar: "Abin sani kawai, Majibincinku Allah, da Manzon Sa..."
Haka kuma yazo cikin tafsirin Arrazi, Juz'i na 12, Shafi na 26:
روي عن أبي ذر رضي الله عنه أنه قال: صليت مع رسول الله (صلى الله عليه وآله) صلاة الظهر، فسأل سائل في المسجد فلم يعطه أحد فرفع السائل يده إلى السماء وقال: اللهم أشهد إني سألتك في مسجد الرسول (صلى الله عليه وآله) فما أعطاني أحد شيئاً، وعلي كان راكعاً، فأومأ إليه بخنصره اليمنى، وكان فيها خاتم فأقبل السائل حتى أخذ الخاتم بمرأى النبي (صلى الله عليه وآله)... حتى نزل جبريل فقال: يا محمد اقرأ: إنما وليكم الله ورسوله
Ma'ana
Abu Zarri (Allah kara Masa Yarda) ya ruwaito cewa: Nayi Sallar Azahar tare da Manzon Allah (A.S), Sai Almajiri yayi bara a masallaci, babu wanda ya bashi sadaka a masallacin, Sai Almajirin ya daga hannun sa sama ya ce: "Yaa Allah ka zamo Shaida na rokeka a cikin masallacin Manzon ka (A.S) Babu wanda ya bani wani abu," a wannan lokacin Aliyu ya yi Ruku'i, Sai Aliyu ya Nuna wa Almajirin 'DanyatsanSa na dama wanda acikin sa ne akwai zobe, Almajirin ya matso ya cire zoben, da Manzon Allah (A.S) Ya hango, sai Mala'ika Jibrilu Ya sakko Yace, "Ya Muhammad! Ka karanta: (Abin sani kawai Majibincinku Allah da Manzon Sa....)
Sannan kuma Malam Suyudi ya kawo cikin littafin sa "Durrul Mansuur" Juz'i na 2, shafi na 293, cewa:
عن ابن عباس قال: تصدق علي بخاتمه وهو راكع، فقال النبي (صلى الله عليه وآله) للسائل من أعطاك هذا الخاتم؟ قال: ذاك الراكع، فأنزل الله: إنما وليكم الله ورسوله
Ma'ana
Daga Ibn Abbas Yace: Aliyu ya yi sadaqa da Zobensa a lokacin yana cikin Ruku'i. Sai Manzon Allah (A.S) Yace da Almajirin, "Waye Ya baka wannan Zoben?" Ya amsa da cewa, 'Wancan dake Ruku'i.' Sai Allah Ya saukar da (Abin sani kawai Majibincin ku Allah da ManzonSa...)
Malam Zamashkari kuma cewa ya yi:
الآية نازلة في علي باتفاق أكثر المفسرين
Ma'ana
Ayar Wilaya ta sauka ne akan Aliyu bisa ga Ittifaqin Mafi akasarin Malaman Tafsiri.
Yazo cikin Littafin Tafsir na Malam Aloosi, juz'i na 6, shafi na 167, cewa:
وغالب الأخبار بيّن على أنها نزلت في علي كرم الله تعالى وجهه
Ma'ana
Sannan Mafi yawan labarai sun bayyana cewa (Ayar Wilaya) ta sauka ne akan Aliyu, Allah Ya daukaka Fuskarsa.
Ga kuma jerin Malaman Tafisirn Sunnah da suka tabbatar da cewa Ayar ta sauka ne akan Imam Ali (A.S) kamar yadda muka kawo wasu a sama daga cikin Malaman Sunnah:
-Ibn Kathis cikin tafisirin sa, Juz'i na 2, Shafi na 64.
-Tafsir na Tabari, Juz'i na 6, Shafi na 186
-Tafsiin Qurdubi, Juz'i na 2, Shafi na 47
-Asbabun Nuzul na wahidi, shafi na 113
-Tafsirin Shaukani, juz'i na 2, shafi na 53
-Tafsiri na Ibn Jauzi, 'zaadal Masir' Juz'i na 2, shafina 283
-Tafsirin Nasfi, Juz'i na 1, shafi na 289.
Duk da irin wadannan ingantattun hujjojin da ke tabbatar da cewa ayar wulaya ta sauka ne akan Imam Ali (A.S) bai hana Shugaban wahabiyawa Ibn Taimiyyah bayyana qiyayyar su ta hanyar karyata ruwayoyi ba. Malamin na cewa:
وقد وضع بعض الكذابين حديثاً مفترى أنّ هذه الآية نزلت في علي لما تصدق بخاتمه في الصلاة، وهذا كذب بإجماع أهل العلم
Ma'ana
Wasu Makaryata Masu Kirkirar Hadisi sun kirkiri hadisin akan cewa wannan Ayar (Ayar Wilaya) ta sauka ne akan Aliyu da Ya bada sadakar Zoben sa Yana Sallah, Wannan Karyace bisa ga Ijma'in Ma'abota Ilimi (Malamai).
Yanzun bamu san tsakanin Magabatan Sunnah da Sahabban da suka ruwaito Hadisin cewa Ayar ta sauka ne akan Imam Ali (A.S) da Ibn Taimiyyah waye makaryacin ba?! A zahiri Wannan na nuna tsananin Kiyayyar Wahabiyawa ga Ahlul Baiti (A.S) suna fito na fito da duk wata falalar Imam Ali (A.S) ko wani daga cikin zuriyar Sa Tsarkaka.
وصلى الله على سيدنا محمد وأهل بيته الطيبين الطاهرين